Tattaunawar Palasdinawa da Isra'ilawa cikin makonni hudu

Shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Amurka da wasu manyan kasashen duniya sun bukaci Isra'ilawa da Palasdinawa da su sake dawowa da tattaunawar zaman lafiya cikin makonni hudu

Sanarwar kasashen ta deba lokaci ga Isra'ilawa da kuma Palasdinawa da su sake dawowa da tattaunawa cikin makonni hudu, su kuma cimma wata yarjejeniyar zaman lafiya zuwa karshen shekarar 2012.

Amma sanarwar bata ce komai ba dangane da matsugunan da yahudawa 'yan kama wuri zauna suke giniwa.

Haka kuma sanarwar ba tayi kira ga samar da wata kasa ta Palasdinawa ba, tare da yin la'akari da iyakokin da aka shata kafin yakin shekarar 1967,

Wadannan kuma sune irin sharuddan da Palasdinawan suke cewa lallai sai an cimma su , kafin su dawo da duk wata tattaunawa.

Wasu jami'an Palasdinawa dai sun bayyana wannan kira na Amurka da cewar bashi da wani amfani.

Amurkawa dai sun lashi takobin hawa kujerar naki a madadin Isra'ila, dangane da bukatar da Palasdinawa suke shigar.

Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya dai zai gana a ranar litinin domin ya soma duba bukatar da Palasdinawa suka shigar, zai kuma dauki wasu 'yan makonni yana yin wannan aiki