Shugabar IMF ta gargadi kasashen duniya

Christine Lagarde Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ba lallai bane asusun bada lamuni na duniya ya iya tunkarar tabarbarewar tattalin arzikin duniya a nan gaba saboda rashin isassun kudade

Shugabar asusun bada lamuni na duniya Christine Lagarde ta ce asusun zai bukaci karin kudi sosai, idan har matsalar tattalin arziki ta munana.

Christine Lagarde ta ce ikon asusun na bada bashin da ya kai dala billiyan dari hudu, a halin yanzu babu matsala, to amma ba zai isa ya biyan dukkanin bukatun kasashen turai dake cikin matsalar basussuka ba, idan al'amarin ya sake tabarbarewa.

Kodayake ta bayyana fatanta na shawo kan lamarin.

Hukumar bada lamunin ta duniya dai na samun kudadenta ne daga karo karon kudi daga wasu mambobin kasashe su ashirin.

A lokacin rikicin kafofin kudade a shekarar 2009, mambobin kasahen su ashirin suka yanke shawarar kara kudaden da suke bayarwa sosai.

Dole ne kuma su sake tunanin yin hakan, idan har kudaden zasu taka mahimmiyar rawa wajen farfado da tattalinn arzikin duniya