Mahmoud Jibril ya roki majalisar dinkin duniya

Babban Sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon
Image caption Gwamnatin rikon kwaryar kasar Libya ta nemi majalisar dinkin duniya ta saki dukiyar kasar da aka rike a lokacin yaki

Fira Ministan majalisar rikon kwaryar kasar Libya Mahmoud Jibril, ya yi kira ga Majalisar dinkin duniya da ta sako dukkanin dukiyar kasar da aka kwace ga gwamnatinsu.

Mr. Jibril na jawabinsa na farko ne a hukumance ga taron majalisar dinkin duniya da ake yi a birnin New York.

Ya ce ya kamata a saki dukiyar kasar da aka kwace ba tare da bata lokaci ba.

Ya kuma yi kira ga kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniyar da ya janye takunkumin da aka sanya a dukiyar kasar, yana mai cewa Gwamnatin Gaddafi ta kau, kuma yanzu lokaci ne da za'a maida hankali wajen sake gina kasar da kuma kyautata makomar rayuwar matasan da suka yi yakin juyin juya hali

Fira Ministan ya kuma ce gwamnatinsu zata baiwa kasashen duniya duk irin goyan bayan da suke bukata sabanin gwamnatin Gaddafi a cewarsa