Wangari Maathai ta rasu a Nairobi

Wangari Maathai Hakkin mallakar hoto internet
Image caption Wangari Maathai ta kasance mace ta farko a Afirka data karbi kyautar Nobel

Mai rajin kare muhalli da hakkin mata a kasar Kenya Wangari Maathai, ta rasu a asibitin dake Nairobi inda ta sha fama da cutar sankara ko cancer.

Wangari Maathai dai ita ce mace a Afirka ta farko da ta samu kyautar Nobel na zaman lafiya a shekarar 2004.

Ta taba zamantowa mamba a majalisar dokokin kasar ta Kenya, kuma ta zamanto karamar mamba a gwamanatin kasar. Ta rasu tana da shekaru 71 a duniya.

Ta soma taka Rawa a matsayin mai rajin kare muhalli bayan data shuka bishiyu a bayan gidanta, kuma ta kafa wata kungiya da ake kira Green Belt Environment a shekarun 1970, akasarin 'yan kungiyar mata ne wadanda ke yaki da illar sare dazuka.

An dai sha tsare ta a Karkashin tsohuwar gwamnatin Daniel Arap Moi.