Ana zargin mutane shida da aikata ta'addanci a burtaniya

Ana zargin mutanen uku Irfan Khalid da Ashik Ali wadand a dukkaninisu shekaunsu ashirin da shida da haihuwa da kuma dan shekaru talatin Ifan Nasir da cewar 'yan kunar bakin wake ne.

An dai yi zargin cewar a watanni taran da suka gabata sun shirya kai harin bam a birtaniya da kuma kirkiro da wani abu mai fashewa.

'Yan sanda sunyi ikirarin cewar Irfan Khalid da Irfann Nasir sun sami horon aikata ta'addanci a kasar Pakistan.

Ana kuma zargin wani mutum daban da ake kira Rahin Ahmed mai shekaru ashirin da biyar da haihuwa da taimkawa wasu wajen zuwa kasar pakistan domin su sami horon ta'addanci da kuma zuba jarinsu a harkar ta'addanci.

Ana kuma zargin dan uwan Ashik Ali wato Bahadir Ali da tara kudade domin aikata ta'addanci da kuma kin bayar da bayanai game da ta'addancin ga 'yan sanda, zargin da ake yiwa mutum na shida wato Mohd Rizwan.

A yanzu dai ana yiwa wani mutum daban tambayoyi bisa wadansu zarge zarge