Jami'o'i za su kara kudin makaranta - ASUU

Image caption Taswirar Najeriya

A ranar Talata ne yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai da malaman jami'a suka fara a Najeriya a jiya ya shiga rana ta biyu.

Malaman na kokarin jawo hankalin gwamnatin tarayyar kasar ne domin ta aiwatar da wata yarjejeniyar baiwa jami'ion kasar Karin kudaden gudanar da su wadda ta sanyawa hannu shekaru ukku da suka wuce.

Da dama daga cikin 'yan Najeriya na ganin yajin aikin da malaman kan yi ba ya yin wani tasiri wajen shawo kan matsalolin da ke tattare da ilimin jami'a a kasar.

Shugaban kungiyar malaman jami'a reshen Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Dakta Lawal Abubakar Argungu ya shaidawa BBC cewa yajin aikin a wannan karon ya zama wajibi domin tsarin jami'a a kasar na gab da durkushewa.

Ya ce jami'o'i a Najeriya ba su da kudaden gudanarwa abun da kuma ke janyo tabarbarewar hakar Illimi.

Dakta Lawal ya ce muddin gwamnati ba ta cika alkawarin da ta yiwa malaman ba, shugabannin jami'a za su kara kudin makaranta, abun da kuma ya ce zai gaggare 'yan 'yan talakawa da dama.