Papandreou zai gana da Merkel a kan karin tallafi

Image caption Shugabar, gwamnatin Jamus Angela Merkel da Fira Ministan Girka George Papandreou

Fira Ministan Girka, George Papandreou, zai gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, kafin Majalisar Dokokin kasar ta Jamus ta kada kuri'a a kan ko kasar za ta goyi bayan ba da karin tallafi ga Girkar.

Tun a watan Yuli ne dai shugabannin kasashen da ke amfani da kudin euro suka amince da tallafin.

Tuni dai darajar hannayen jari ta daga a farkon bude kasuwannin hannayen jari a Asiya, yayin da ake fatan an gano bakin zaren warware matsalar bashin da ta dabaibaye nahiyar ta Turai.

Sai dai jami'ai sun ce ya yi wuri a bayyana cewa an samo wata dabara kwakkwara.

Shugaba Obama na Amurka ya ce abin da ke faruwa a Turai yana razana kasuwannin duniya:

Mista Obama ya ce kasashen Turai na fuskantar rikicin tattalin arziki wanda ke razana duniya.

Ya ce sai dai suna kokarin daukar matakin da ya dace, ko da ya ke suna yin nauyin jiki wajen daukar matakin.