An fara shari'ar likitan Michael Jackson

Hakkin mallakar hoto Getty

Lauyan dake kare likitan Michael Jackson ya shaidawa wata kotu a Los Angeles cewar mawakin shi ne musababbin mutuwar kansa da kansa.

Likitan Michael Jackson din , Conrad Murray ya musanta kisan kai ba da niyya ba.

Lauyansa ya ce a lokacin da Dr Murray ba ya nan, shahararren mawakin zamanin ya sha wani hadin maganin bacci wanda ya haddasa abinda ya bayyana a matsayin wanda ya rikita jikinsa baki daya, ya kuma kashe shi nan take.

Tun farko babban mai gabatar da kara, David Walgren, ya zargi Dr Murray da babban sakaci wajen kula da mawakin.