Bill Gates ya na ziyara a Nigeria

Bill Gates
Image caption Bill Gates

Hamshakin attajirin nan Ba-Amurke, Bill Gates, ya na wata ziyara a Najeriya domin sa ido a kan shirin yaki da cutar shan inna.

Gidauniyar Bill da Melinda Gates dai tana daukar nauyin tallafa wa wannan shiri na yaki da cutar ta shan Inna.

A makon jiya ne aka kaddamar da wani sabon shiri yin allurar riga-kafin cutar.

A bana kadai cutar ta kama mutane akalla talatin a wasu jihohin kasar da suka hada da Borno, da Jigawa, da Kano, da Kebbi da Sokoto da kuma Yobe.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da Bill Gates ya ziyarci Nigeria domin sa ido akan shirin na yaki da cutar shan Inna.