Za'a tattauna akan bukatar Falasdinu

Image caption Shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas

Membobin Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya za su gana a gobe Laraba, akan bukatar Falasdinu na nema kasa mai cin gashin kanta.

A bayannan taron ne bayan da Wakilan kasashe su ka yi wata ganawa ta sirri.

Shugaban Mahmoud Abbas ne ya bayyana bukatar Falisdinawa ga Majalisar a ranar juma'ar da ta gabata, duk da barazar da Amurka ta yi, ta hawa kujerar naki.

A ranar Laraba ne ake sa ran kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, zai mika, bukatar Falasdinu ga kwamitin sa mai kula sabbin membobi.

Jami'an diplomassiya dai na ganin cewa sai an dauki kamar wata daya kafin Majalisar ta kada kuri'a akan bukatar da Falasdinu ta gabatar ma ta.

Falasdinawa dai nu bukatar goyon bayan kasashe tara ne, kuma idan ba su samu hakan ba, ba za'a iya kada kuri'a game da bukatar tasu ba.

Ita ma dai Amurka ba za ta sha kunyar hawar kujerar naki ba, saboda ba'a samu kasashen da ake bukata ba.

Kasashen Gabon da Nigeria da kuma Bosnia ne ake ganin kamar kasashen da za'a yi samun nasara da kuri'unsu, kuma a yanzu haka za su rika fuskantar matsin lamba ne daga Amurka da kuma Falasdinawa a 'yan kwanaki masu zuwa saboda neman goyon baya.