Amurka ta soki Isra'ila kan gina gidaje a birnin Kudus

Image caption Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, ta yi suka a kan shawarar da hukumomin Isra'ila suka yanke ta amincewa da ginin gidaje dubu daya da dari daya a Gabashin birnin Kudus, inda ta mamaye.

A cewarta: "Mun yi amanna wannan sanarwa ta gwamnatin Isra'ila wadda ta amince da ginin jerin wasu gidaje a Gabashin birnin Kudus zai yi kafar ungulu ga yunkurinmu na farfado da tattaunawa tsakaninsu da Falasdinawa."

Misis Clinton ta kuma ce akwai bukatar bangarorin biyu su guji aikata duk wani abin da ka iya jawo ta da jijiyar wuya.

Falasdinawa dai sun ce wajibi ne Isra'ila ta dakatar da gine-ginen matsugunan Yahudawa kafin su amince da tattaunawa.

Neman goyon baya

A ranar Laraba ne ake sa ran kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, zai mika, bukatar Falasdinu ga kwamitin sa mai kula sabbin membobi.

Jami'an diplomassiya dai na ganin cewa sai an dauki kamar wata daya kafin Majalisar ta kada kuri'a akan bukatar da Falasdinu ta gabatar ma ta.

Falasdinawa dai nu bukatar goyon bayan kasashe tara ne, kuma idan ba su samu hakan ba, ba za'a iya kada kuri'a game da bukatar tasu ba.

Ita ma dai Amurka ba za ta sha kunyar hawar kujerar naki ba, saboda ba'a samu kasashen da ake bukata ba.

Kasashen Gabon da Nigeria da kuma Bosnia ne ake ganin kamar kasashen da za'a yi samun nasara da kuri'unsu, kuma a yanzu haka za su rika fuskantar matsin lamba ne daga Amurka da kuma Falasdinawa a 'yan kwanaki masu zuwa saboda neman goyon baya.