Ivory Coast ta kaddamar da hukumar hada kan kasa

ivory coast Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taron ministoci akan zaman lafiya a Ivory Coast

Kasar Ivory Coast ta kaddamar da wata hukumar neman gaskiya da sasantawa domin kokarin dinke barakar kabilanci da ta addinin data haddasa mutuwar mutane akalla dubu uku a tashin hankalin da ya biyo bayan zabe a wannan shekarar.

Da farko dai hukumar za ta saurari ba'asi daga wadanda rikicin ya shafa, wadanda daga baya kuma za su shiga cikin wasu tarukan jama'a tare da wadanda aka zarga da aikata ta'asar.

Shugaban kasar da aka hambarar, Laurent Gbagbo, wanda kin da yayi na karbar shan kaye a zaben a bara, ya haddasa tashin hankalin , zai fuskanci shara'a tare da na hannun damarsa da yawa.

Masu sukar hukumar neman gaskiyar sun yi korafin cewar babu wani daga cikin mutanen Shugaba Alassane Quttara da aka tsare.