Kotun Faransa ta ki amincewa da bukatar Rwanda

agather
Image caption Tsohon shugaban Rwanda da Uwargidansa

Kasar Rwanda bat a yi nasarar samun Faransa ta mika mata matar tsohon Shugaban kasar Rwandan, Agathe Habyarimana.

Ana zargin ta ne da kasancewa babbar makitsiyar kisan kare dangin 1994 a Rwanda, kisan da ya biyo bayan kisan mijinta.

Wata kotun daukaka kara ta Faransa ta yanke hukuncin cewa zargin da ake mata na kisan kiyashi da kuma cin zarafin bil adama, ba shi da makama.

Da take marhabin da hukuncin, Misiz Habyarimana ta ce a koyaushe tana da amannar cewar Faransa za ta kare ta

Ta ce, “Ina farin ciki, ina murna, kuma a kodayaushe ina da kwarin guiwa a kan tsarin shari'ar Faransa.”

Rwanda ta ce a halin yanzu tana son Faransa ta gurfanar da ita da kanta da kanta.

Mutane dubu dari takwas ne aka yi kiyasi, galibi ‘yan kabilar Tutsi marasa rinjaye da ‘yan gwagwarmayar kabilar Hutu suka kasha, bayan da aka kasha.

Shugaba Habtarimana dan kabilar Hutu a wani hadarin jirgin sama.