Za'a kada kuri'a a kan Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zangar adawa da gwamnati a Syria

Burtaniya da wasu mayan kasashen Turai da ke kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, sun fito da wani kudiri a Majalisar da zai yi barazanar sanya takunkumi a kan Syria a maimakon sanya takun-kumi kai tsaye.

Anan dai ganin wannan matakin zai shawo kan kiki kakan da aka yi tsakanin kasashen Turai game da irin matakin da za'a dauka a kan Syria saboda yadda gwamnatin kasar ke cin zarafin masu zanga-zangar adawa da ita a kasar.

Jami'an Diplomasiyya dai sun ce Majalisar za ta kada kuri'a game da kasar a karshen wannan mako.

A karshen watan daya gabata ne kasashen Turai da ke kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Amurka su ka fito da wani kuduri da ke kira da a kakkabawa Shugaban Syria, Bashar al Assad da na kusa da shi takun-kumi.

Ammai sai kudurin ya fuskanci turjiya daga wasu daga cikin membobin kwamitin, musamman ma kasar Rasha wadda ke da iko hawan kujerar naki wajen kada kuri'a.

A yanzu haka dai kasashen sun kara yiwa kudurin garon bawul ne, inda kawai ya kunshi barazanar sanyawa gwamnati Shugaba Assad, takunkumi, idan bai dakatar da ayyukan soji akan fararen hula a kasar ba.

Jami'an diplomasiyya sun nuna kwarin gwiwa, a kan sabon kudurin wadda ake ganin za'a kada kuri'a akan sa a karshen wannan makon.

Sauran kasashen da basa so su ga an sanyawa Syria takunkumi sun hada da China wadda ke da ikon hawan kujerar naki da kuma kasashen Indiya da kasar Afrika ta kudu da kuma Brazil.