Burtaniya na adawa da sabon harajin bankuna

Bankuna a Turai
Image caption Jama'a na adawa da wasu matakan da ake dauka

Burtaniya ta ce za ta yi adawa da sabon tsarin haraji kan cinikin hukumomin kudi da Tarayyar Turai ke son bullowa da shi a tsakanin kasashen Tarayyar.

Harajin zai samar da fan biliyan 50 a shekara kuma za a fara aiki da shi ne a shekara ta 2014.

Shugaban tarayyar Jose Manuel Barroso ya ce wajibi ne bankuna "su bayar da tallafi " a daidai lokacin da Turai ke fuskantar "babban kalubale".

Burtaniya ta ce ba ta adawa da harajin a hukumance, amma idan aka sanya shi a fadin duniya baki daya.

Haraji kan cinikayya na bukatar amincewar Burtaniya domin ya yi aiki a Tarayyar ta Turai.

Tarayyar ta ce idan Burtaniya ta hau kujerar naki kan batun, za ta aiwatar da shi a tsakanin kasashen da ke amfani da kudin euro.

Mr Barroso ya kara da cewa "ana bukatar sake duba yarjejeniyar Lisbon" domin amincewa da matakan farfado da tattalin arziki.