An kama masu safarar magunguna a masana'antar Boeing

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kamfanin Boeing na kerawa sojin Amurka, jiragen yaki

Hukumar tsaron cikin gidan Amurka wato FBI ta kai samame inda ta cafke mutane talatin da bakwai da ake zarginsu da safarar magunguna a wata masana'antar kera jirage na kamfanin Boeing.

Wadanda ake tsare da su, sun hada da tsaffin ma'aikata da wandanda ke aiki a masana'antar da ke kusa da Philadelphia wadda ke kera jiragen sama da masu saukar angulu wa sojin Amurka.

Wasu ma'ikatan Boeing ne dai su ka kai masa tsegumin safarar magungunan da ake yi a masana'antan sa.

Shugabanni kamfanin ne dai su ka gayyaci, hukumar tsaron cikin gida ta FBI, inda kuma suka turo jami'an leken asirin masana'antar.

Masana'antar dai na kera jirge masu saukar angulu na Chinook da kuma jiragen yaki da Amurka ke amfani da su a Afghanistan.

Wadanda ake tsare da su, sun hada da mata da maza ne wadanda shekarun basu haura arba'in ko hamsin ba.

Ana dai zargin su ne da safarar magungunan da likitoci ke rubutawa mutane.

Boeing dai ya ce safarar magungunan da ake yi a masana'antar bai shafi ayyukansa ba na kera jirage.