'Yan bindiga sun bude wuta a Kamaru

biya Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Shugaban Kamaru Paul Biya

Wasu 'yan bindiga sun bude wuta a Duala, babban birnin kasuwancin kasar Kamaru, inda suka kashe akalla mutun guda.

Rahotanni sun ce 'yan bindigar suna sanye ne da kayan soji, suna kuma dauke da kwalayen da ke neman lalle sai Shugaba Paul Biya ya sauka daga mulki.

Ana dai shirin yin zaben shugaban kasa ranar tara ga watan gobe na Oktoba.

Shugaba Biya, wanda shekaru kusan talatin ke nan yana kan mulki, shi ne ake sanya ran zai lashe zaben.

A shekara ta 2008 ya sauwa tsarin mulkin kasar don kawar da duk wani tarnaki ga yawan wa'adin da zai iya kasancewa a karagar mulki.