Amurka ta nemi Masar ta dage dokar ta-baci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sakatariyar harkokin kasashen wajen Amurka, Hillary Clinton

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce ya kamata gwamnatin mulkin soja ta Masar ta dage dokar ta-bacin da ke aiki a kasar ba tare da bata lokaci ba.

A cewarta Amurka za ta so ta ga an dage dokar ta-bacin kafin watan Yunin badi, lokacin da aka tsara yin hakan:

"Majlisar kolin Masar din ta ce za ta iya dage dokar ne a shekarar 2012; amma muna fatan ganin an yi hakan kafin lokacin saboda a ganinmu muhimmin mataki na tabbatar da doka da oda kuma samar da yanayin da za a gudanar da zabuka irin na dimokuradiyya." In ji Clinton

Misis Clinton ta yi wadannan kalamai ne bayan wata ganawa da ta yi da ministan harkokin waje Masar Muhammad Amr a Washington.

Gwamnatin rikon kwaryar ta Masar dai ba ta jima da kara tsawaita dokar ta-bacin ba wadda hambararren shugaban kasar Hosni Mubarak ya kaddamar.

Gyaran doka

Wani kawancen siyasa a Masar a karkashin jagorancin kungiyar 'yan uwa Musulmi, wato Muslim Brotherhood, ya yi barzanar kauracewa zabubbukan da ke tafe a kasar in har ba a yi gyaran fuska ga dokar zabe ba.

Kawancen mai suna Democratic Alliance ya nuna rashin gamsuwa ne da wani tanadi a dokar zaben wanda ya ware sulusin kujerun majalisar dokoki ga 'yan takarar indifenda.

Kawancen ya debawa gwamnatin mulkin sojin kasar wa'adin ranar Lahadi 2 ga watan Oktoba ta biya musu bukatunsu.

Ana sa ran za a gudanar da zabukan majalisun dokoki daki-daki a kasar kama daga 28 ga watan Nuwamba.