Jamus ta amince da karin tallafi ga Girka

Angela Merkel Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gudummawar Jamus na da matukar muhimmanci

Majalisar dokokin kasar Jamus ta amince da gagarumin rinjaye domin fadada asusun tallafawa kasashen da ke fama da matsalar kudi irinsu Girka da Portugal.

Ana yi wa kuri'ar kallon wani zakara gwajin dafi kan ikon shugaba Angela Merkel, ganin yadda wasu daga cikin gwamnatin hadakarta suka ce ba za su goyi bayan kudurin ba.

Da dama daga cikin 'yan kasar na dari-dari da kara zuba kudi domin ceto kasashen da ke cikin gammayyar euro irinsu Girka.

Ana zanga-zanga a birnin Athens na Girka inda masu sa'ido ke ziyara domin tattauna yadda za a bayar da karin tallafin.

'Yan majalisa 523 ne suka amince da kudurin, 85 suka yi watsi da shi yayin da uku suka kaurace a majalisar ta Bundestag mai wakilai 620. Mambobi tara ba su halarci zaman ba. Ana sa ran kudurin zai samu amincewar majalisar dattawan kasar ranar Juma'a inda za a kada kuri'a a kai.

Dukkan kasashe 17 da ke amfani da kudin euro dole ne su amince da fadada asusun wanda zai samar da kudade kimanin euro biliyan 440 (fan biliyan 383).

Kawo yanzu 10 daga cikinsu sun amince da matakin.

A matsayinta na wacce ta fi kowacce kasa karfin tattalin arziki a Turai, gudummawarta ga Asusun tabbatar da harkokin kudi a Turai (EFSF) zai karu daga euro biliyan 123 zuwa biliyan 211.

Karin bayani