Pakistan ta gargadi Amurka akan masu fafutuka

Yusuf Raza Gilani Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Firaministan Pakistan, Yusuf Raza Gilani

Firaministan Pakistan, Yusuf Raza Gilani, ya ce duk wani yunkuri da Amurka za ta yi na matsa wa Pakistan ba zai yi nasara ba.

Firaminista Gilani yana jawabi ne ga wani taro na musamman na shugabannin addini da na siyasa da aka kira cikin gajeren lokaci, bayan da Hafsan Hafsoshin Sojin Amurka, Adimral Mike Mullen ya zargi Pakistan da goyon bayan masu fafitika.

Wakilin BBC ya ce, "Firaminista Gilani ya ce dole ne Amurka ta daina dorawa wasu laifukanta, kuma ta daina zargin Pakistan da haddasa fitina a wasu kasashe. Har ila yau Firaministan ya bayyana aniyar Pakistan na kare martabarta.