Nijar ba za ta mika Sa'adi Gaddafi ba

Sa'adi Gaddafi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sa'adi Gaddafi ya jagoranci Hukumar Kwallon Libya a baya

Fira ministan Nijar Brigi Rafini ya ce kasar ba za ta mika dan Kanal Muammar Gaddafi, wato Sa'adi Gaddafi ga hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa Interpol ba.

Hukumar 'yan sanda ta duniya, Interpol, ce dai ta fitar da sammacin kama Sa'adi Gaddafi, dan tsohon shugaban Libya, Kanar Mu'ammar Gaddafi.

Interpol tana zarginsa ne da aikata wasu laifuka a lokacin da yake jagorancin hukumar kwallon kafar kasar.

Sai dai Nijar ta ce babu tabbacin cewa Sa'adi zai samu shari'a mai adalci a kasar Libya.

Interpol ta ce ta fitar da sanarwa - wadda ke daidai da ayyana cewa mutumin yana cikin wadanda aka fi nema a duniya ruwa a jallo.

Kuma sabuwar gwamnatin wucingadi ta Libya ce ta nemi a yi hakan.

Gwamnatin jumhuriyar Nijar dai ta tabbar cewa Sa'adi Gaddafi yana cikin Nijar din.

Tuni dama Hukumar Interpol ta fitar da irin wannan sanarwa a kan tsohon jagoran jami'an ayyukan sirri na Libyar, Abdullah Al Senussi.