Najeriya za ta sake sabon katin shaidar dan kasa

Image caption Taswirar Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta sake yi wa al'ummarta katin shaidar zama dan kasa irin na zamani wanda zai kunshi muhimamman bayanai a kan kowane dan kasar.

Gwamnatin har wa yau ta ce kuma za a iya ganin bayanan ta hanyar amfani da na'urar komfuta.

Ta ce dai ta ce katin zai taimaka wajen samar da bayanai a kan 'yan kasar, tare da inganta harkar tsaro.

A baya dai gwamnatin Najeriyar ta yi wani yunkurin yi wa 'yan kasar katin shaidar zama dan kasa, inda aka kashe dubban miliyoyin naira.

Wannan yinkuri nata ya cije yayin da fiye da rabin 'yan kasar ba su samu katin ba.

Majalisar zartawar kasar wadda ta bayyana cewa za'a sabon katin ta ce kashin farko dai ana sa ran zai ci fiye da naiya miliyan talata.

Za'a dai fara katin ne a wannan shekara, kuma ana sa ran za'a kammala shi ne cikin shekaru uku.