Najeriya za ta kafa kwamitin kawar da cutar Polio

Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi alkawarin kafa wani kwamiti na musamman wanda zai kawar da cutar shan inna a kasar nan da shekaru biyu masu zuwa.

Mr. Jonathan dai na magana ne lokacin ziyarar hamshakin attajirin nan Bill Gates a babban birnin kasar Abuja.

Najeriya, daya daga cikin kasashe hudu na duniya wadanda suka rage da cutar ta polio

Najeriya dai ta samu nasarar yakar cutar da kashi 95 cikin dari a shekara ta 2009.

Amma sai cutar ta sake kunno kai a bana a wasu jahohi shida na kasar.

Dokta Adamu Isa, wani likita wanda ya kware a yaki da cutar ya ce lallai sai gwamnati ta hada da al'umma za ta samu nasarar yakar cutar.

"Dolene a yi aiki tare da shugannin al'umma da na gargajiiya da na addini wajen wayar da kan jama'a.

Su ne su ka san matsalolin al'ummarsu, kuma sune za su iya taimakawa wajen samar da nasara da yaki da cutar." In ji Dokta Adamu Isa.