Amurka ba za ta janye jakada a Syria ba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sakatariyar kasashen wajen Amurka, Hillary Clinton

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta soki harin da aka kaiwa jami'an diplomasiyar Amurka a Syria inda har aka jefi jakadanta da duwatsu da kuma tumatir.

Misis Clinton ta ce wani yinkuri ne na yin barazana ga jakadun kasashen wajen ta hanyar tayar masu da hankali, inda kuma ta ce kasar ba ta da niyyar janye jakadar ta a Syria.

Magoyan bayan shugaban Syria sun jefi jakadan Amurka a Syria Robert Ford da tumatur da `duwatsu a lokacin da ya ke ganawa da jami'an 'yan adawa a birnin Damascus.

Jakadan dai ya kama aiki ne a kasar a watan Junairun wannan shekara.

Misis Clinton dai ta ce harin da aka kaiwa jami'an diplomasiyya a Syria wani barazana ne ga jami'an diplomasiyyar kasashen waje, domin su daina sa'ido a irin ayyukan da gwamnatin kasar ke yi musamman ma na cin zarafin masu zanga zanga da adawa da gwamnatin kasar.

Gogaggen dan siyasa Hassan Abdul Azim ya ce akalla masu zanga-zanga 100 ne su ka yi kokarin kutsa kai ofishinsa a lokacin da Mr Ford ya isa wurin, sannan su ka yi garkuwa da su a ciki.

Jami'an Amurka sun ce lamarin ya lalata motocin ofishin jakadancin, amma ba abinda ya samu Mr Ford.

Tunda farko dai Syria ta zargi Amurka da ingiza jama'a su yiwa sojojinta bore.