An kashe wani jagoran al-ka'ida Anwar Al-Awlaki

Anwar Al-Awlaki Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tuni shugaba Obama ya bada umarnin a kashe Al-Awlaki

Jami'ai a Amurka da Yemen sunce an kashe daya daga cikin masu fada aji mafiya karfi a kungiyar al-ka'ida, wanda kuma malamin Musuluncin ne haifaffen Amurka, Anwar Al-Awlaki.

Sun ce jiragen yakin Amurka da kuma jirage marasa matuka a Yemen sun kai wa jerin gwanon motocinsa hari.

Tun farko rahotanni sunce an kai farmakin ne a tsaunukan da ke da nisan kilomita 140 gabas da birnin Sanaa babban birnin kasar.

Hakan ya biyo bayan wani umurnin da Shugaba Obama ya sanya wa hannu a bara na nemowa da kuma kashe Awlaki, wanda dan kasar Amurka ne.

An zargi Anwar Awlaki wanda dan asalin Yemen ne da hannu a hare-hare da yawa, da suka hada da wani yunkuri na tarwatsa wani jirgin da ke kan hanyarsa ta zuwa Detroit a lokacin Kirsimatin shekara ta dubu 2009.

Ana zarginsa da laifuka da dama

An kashe Al-Awlaki ne a wani hari ta sama da Yeman da Amurka suka kitsa.

Anwar Al Awlaki ya yi suna ne ta laccocinda ya ke yi da kuma ra'ayoyinsa da ake wallafawa ta shafukan internet, inda ya ke yin kira da akai hare-hare a kan wadanda ya kira maikya addinin musulunci.

An kuma san shi da kushe shugabanin kasahen Larabawa. A wata lacca da ya gabatar ya kakkausar suka a gare su:

"Wadannanan sarakunan da shugabannin kasashen Larabawa basu cancanci shugabancin ko wacce kasa ba. Kai ba su ma dace da kiwon garken awaki ba," a cewarsa.

Sanarwar kisan sa babu shakka wata babbar komabaya ce ga kungiyar Al-ka'ida tun bayan kisan Osama bin Laden a watan Mayu.

A bara ne Shugaban Amurka Barrack Obama ya bada wani umarni mai cike da kace-nace na hallaka Al-Awlaki duk inda aka ganshi.

Ana dorawa Al Awlaki lafin hare-haren da wasu suka kai a Amurka da Turai.

Ga misali ana ganin shi ne ya karfafawa wani sojan Amurka, Manjo Hassan Nidal gwiwa, har ya kashe wasu abokan aikinsa a Texas.

Hakazalika ana zargin sa da karfafawa wata 'yar Burtaniya Roshorana Chaoudry Gwiwa har ta dabawa dan majalisa Stven Timms wuka don ya goyi bayan harin da aka kaiwa Iraqi.

Al-awlaki yana da kwarjini. Ya kuma nak`anci Turancin Ingilishi don haka zai yi wuya ga Alqaeda ta maye gurbinsa.