Wata kungiya ta ce ita tai harbi a Douala

A Jamhuriya Kamaru, wata kungiya da ta bayyana kanta majalisar koli ta rikon kwarya a Kamaru, wato -Hot Otorite de la tiranzisiyon O Cameroun, ta dauki alhakin harbe-harben bindigogin da aka yi jiya a birnin Douala.

Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin shafinta na Twitter, wanda kuma kakakinta Rev Bertin Kisob ya sawa hannu.

Kungiyar ta ce ta kai wannan hari ne domin sa matsi kan shugaban kasar, Paul Biya wanda ya kwashe shekaru 29 a kan kujeran mulki, na ya yi murabus.

Kungiyar ta kuma lashi takobin ci gaba da kai wasu hare-haren nan gaba domin cimma burinta.