Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Matsayin addinin Musulunci da na Kirista kan tsarin iyali

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jama'a na kayyade iyali saboda dalilai da dama

Bayan da muka saurari matsayin hukumomin lafiya na duniya kan tsarin iyali, a wannan karon mun karkata kan addini ne inda muka ji matsayin addinin Musulunci da na Kirista kan lamarin.

Haka suma likitoci sun baiwa tsarin iyali tasu ma'anar, kamar yadda Dr. Yelwa Usman wata kwararriyar ma'aikaciyar lafiya a Abuja ta bayyana a shirin na mu na wannan makon.

Haka kuma domin jin matsayin addinin Islama kan lamarin Wakilin BBC a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai ya tuntubi Malam Aminu Ibrahim Daurawa, kwamandan hukumar hizba na Jihar Kano.

Wakilin BBC a Kaduna Nurah Muhammad Ringim ya tuntubi Reverend Yunusa Madu Sakataren kungiyar Mabiya Addinin Kirista CAN shiyyar jihar ta Kaduna domin jin yadda addinin Kirista ke kallon tsarin iyali.

To ko anya kuwa al'umma sun gama fahimtar ma'anar tsarin iyali? Wakilin BBC a Jihar Sokoto Haruna Shehu Tangaza ya gana da wasu 'yan Najeriya akan yadda suke ganin tsarin iyali.