Da Pakistan za mu tattauna ba Taliban ba - Shugaba Karzai

Shugaba Karzai Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan

Shugaba Karzai na Afghanistan ya sheda ma wani taron malaman addini cewa hanya daya tak ta samun zaman lafiya a Afghanistan ita ce ta tattaunawa da Pakisan, maimakon kungiyar Taleban.

Shugaba Karzai ya ce ba za a iya gano Majalisar Taliban ba ko kuma jagoranta Mullah Omar.

Ya kara da cewa kshe tsohon shugaban Afghanistan, BurhanuddinRabbani, can baya a wannan watan, kisan da wani dan kunar bakin wake ya yi, bayan da ya yi shigar burtu kamar wakilin zaman lafiya daga kungiyar Taleban.

Shugaba Karzai ya ce hakan ne ya gamsar da shi cewa da Pakistan ne ya kamata a tattauna.