ACF: gwamnonin arewa ku tashi tsaye

A Najeriya kungiyar Dattawan arewacin kasar, ACF ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta amfani da shawarwarin kwamitocin binciken da ta kafa kan rikice rikicen dake afkuwa a yankin arewacin kasar.

Kungiyar wacce ta gudanar da wani taro a Kaduna,ta kuma nuna damuwa a bisa yadda yankin ke fama da koma baya ta fuskar ilimi.

Kiyasi dai ya nuna cewa kimanin yara miliyan goma ne ke gararamba a kan tituna, ba tare da zuwa makaranta ba a arewacin Nigeria.

Kungiyar dai na ganin ya kamata gwamnonin jihohin yankin su tashi tsaye su tinkari aikin dake gabansu.