Hukunce-hukunce masu saba wa juna kan Rwanda

Shugaba Paul Kagame na Rwanda
Image caption Shugaba Paul Kagame na Rwanda

Kotun laifukan yaki ta Majalisar Dinkin Duniya ta yanke hukuncin daurin shekaru talatin a jarun a kan wasu tsaffin ministocin kasar Rwanda bisa hannun da suke da shi a kisan kare dangi a kasar a 1994.

Kotun ta kuma sallami wasu guda biyu, wadanda suka yi ta murna.

Wakilin BBC ya ce, " A karon farko a tarihi, masu shari'a a Kotun ta'asar Rwandar sun sami rabin wadanda ake tuhuma da laifi, rabi kuma ba a same su da laifi ba.

Ministan harkokin waje a lokacin kashe-kashen, Casimir Bizimungu da kuma ministan harkokin waje, Jerome-Clement Bicamumpaka, sun yi ta murnar sakin su da aka yi .

Ministocin biyu da aka daure, Prosper Mugiraneza da tsohon ministan cinikayya, Justin Mugenzi, an daure kowanensu shekaru talatin.