An bukaci gudanar da bincike a kan mutuwar Gaddafi

Gawar Kanar Gaddafi Hakkin mallakar hoto f
Image caption Gawar Kanar Gaddafi

Hukumar kare hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya kamata a gudanar da cikakken bincike game da yadda tsohon shugaban Libya, Kanar Mau'ammar Gaddafi ya mutu.

Hukumar ta bayyana wani hoton da aka dauka ta wayar Salula dake nuni da yadda Mu'ammar Gaddafi ya mutun, a matsayin wani abun damuwa matuka, sannan ya kara da cewar an hana kisan gilla a karkashin dokokin duniya, ta ko wane hali.

Haka ma dai kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta bayyana bukatar gudanar da bincike game da musabbabin mutuwar Kanar Gaddafin.

Amnesty International ta yi kira ga sabuwar gwamnatin wucin gadin Libya ta NTC da ta fito ta yiwa jamaar kasar ta Libya da kuma duniya baki daya, bayani kan yadda aka kashe Kanar Gaddafi.

Kungiyar ta kuma nemi Majalisar wucin gadin Libta ta NTC da ta tabbatar cewa duka wadanda ake zargi da keta Hakkin Bil Adama da laifufukan yaki, ciki har da iyalan Kanar Gaddafi, an mutunta su tare da yi masu adalci a shariar da zaayi musu.