Tsohon jami'in Pakistan ya ce Haqqani na Waziristan

Tutar kasar Pakistan da na Afghanistan
Image caption Tutar kasar Pakistan da na Afghanistan

Tsohon mai baiwa shugaban kasar Pakistan shawara ta fuskar tsaro ya amince cewa masu tada kayar baya 'yan Afganistan dake da alaka da Haqqani na gudanar da al'amuransu daga wasu yankunan kabilun kasar.

Janar Mahmoud Durani mai ritaya, ya shaidawa BBC cewa kusan kowane mutum da yayi fice a cikin masu tada kayar bayan, na arewacin Waziristan ne duk kuwa da kasancewar sojoji a yankin.

Ya kara da cewa dakarun sojin kasar sun kasa shawo kan magoya bayan kungiyar ta Haqqani ne saboda 'yan kungiyar sun fi su yawa.

Yayin da Amurka ke ci gaba da neman a magance masu ta da kayar baya na kungiyar Haqqani, gwamnatin Pakistan a nata bangaren ta dage cewa 'yan kungiyar ba sa zaune a yankin.