Najeriya ta cika shekaru 51 da 'yancin kai

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

A yau ne Najeriya ta cika shekaru 51 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka.

Kuma da safiyar yau din ne shugaban kasar, Goodluck Jonathan yayi jawabi ga 'yan kasar ta kafafen yada labarai na cikin gida.

Jawabin nasa dai na kice da alwashi da kyakkyawar fatan samun cigaba a fuskokin tattalin arziki, makamashi, samar da ayyukan yi da kuma uwa uba magance matsalar tabarbarewar tsaro dake addabar kasar.

Sai dai masu sharhi sunce, shugaban bai bayyana irin hanyoyin da zai bi wajen magance matsalar tsaron ba.

A bana dai ba za'ayi bukuwan fareti na murnar zagayowar ranar 'yancin kai kamar yadda aka saba a kasar ba, saboda dalilai na tsaro.