Jami'an tsaro sun mutu a Syria.

Kamfanin dillacin labarai, mallakin gwamnatin Syria ya ce wasu jami'an tsaro uku sun rasa rayukansu a lokacin da suke kokarin kwance wani bam, kusa da Damascus, babban birnin kasar.

A wani tashin hankalin na daban kuma, wasu 'yan bindiga dake samun goyon bayan 'yan adawa sun bindige wasu fararen hula uku masu aiki da 'yan sanda, a birnin Hama.

A can garin Rastan kuwa inda ake artabu tsakanin sojojin gwamnati da masu zanga-zanga, masu fafutuka ne ke cewa garin ya sake fadawa karkashin ikon gwamnati.

Wani wakilin BBC a yankin, ya ce masu fafutuka suna nuna shakku kan ko za su iya yin nasara a kan gwamnati, ba tare da sun yi amfani da karfi ba.