Masar za ta gyara dokar zabenta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zanga a Masar

Bayan shafe makonni tana fuskantar matsin lamba, da alamu Majalisar mulkin sojin kasar Masar ta amince za ta sauya dokar zaben kasar da ake takaddama akai.

Kafafen yada labarai na gwamnatin kasar sun sanar da cewa, majalisar sojin za ta yi kwaskwarima ga wani sashin dokar zaben, da jam'iyyu siyasa ke fargabar zai iya ba magoya bayan hambararren shugaban kasar Hosni Mubarak, damar sake darewa karagar mulki.

Jam'iyun siyasa a kasar dai sun yi barazanar kauracewa zabukan da aka shirya gudanarwa, muddin ba'a yi gyara a dokar zaben ba.

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin alkahira don neman a gaggauta mika mulki ga farar hula.