"Mubarak bai ce soji su yi harbi ba".Tantawi

Shugaban gwamnatin rikon kwarya ta Soji a kasar Masar ya ce hambararren shugaban kasar, Hosni Mubarak bai taba bada umurni ga sojoji su bude wuta a kan masu zanga zanga ba.

Lokacin da yake jawabi wajen bikin bude wani sabon shirin raya masana'antu a kudancin birnin Alkahira, Fil Mashal Hussein Tantawi ya ce tsakaninsa da Allah, iya gaskiyarsa yake fadi.

A makon jiya ne Fil-Mashal Tantawi ya bayyana a gaban kotun dake yi wa Mr Mubarak shari'a domin bada shaida, amma a bayan idon jama'a.

Shi ne ministan tsaro na gwamnatin Mubarak, kuma ana ganin cewa shaidarsa na da muhimman a shari'ar, inda ake zargin tsohon shugaban kasar da bada umurni ga dakarun gwamnati su bude wuta kan masu zanga zanga.