An kama masu zanga zanga 700 a New York

'Yan sanda a birnin New York na Amurka, sun kama mutane sama da dari bakwai, wadanda su ka datse Gadar Brooklyn yayinda suke zanga-zangar nuna adawa da abun da suka kira babakeren da cibiyoyin kudi ke yi.

Wani jami'i ya ce an kama mutanen ne bayan da masu zanga-zangar suka kawo cikas ga harkar sufuri a kan Gadar daga Unguwar Manhattan. Masu zanga-zangar dai, 'ya'yan wata kungiya ce dake kiran kanta Occupy Wall Street, wadda hadakar masu adawa ne da tsarin jari- hujja.

Suna nuna rashin jin dadinsu ne da abun da suka kira, rashin daidaito a tsakanin al'ummada rashin aikin yi da kuma saka siyasa a yadda ake gudanar da cibiyoyin hada hadar kudi.