Paul Biya na shirin sake lashe zaben Kamaru

biya Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Shugaban Kamaru Paul Biya

A ranar Lahadi mai zuwa ne za ayi zaben shugaban kasa a Kamaru, inda shugaban mai ci a yanzu wato Paul Biya wanda yake kan karagar mulki na kusan shekaru talatin zai fafata da sauran abokan hammayarsa.

Sai da aka yiwa kundin tsarin mulki kasar kwaskwarima inda aka cire batun wa'adin mulki sau biyu kafin shugaban Paul Biya ya samu damar kara tsayawa takara.

Kamar yadda a shekarun baya aka yi zargin magudi tare da tafka kura kurai don Paul Biya ya cigaba da shugabancin kasar, a wannan karon ma 'yan kasar da dama na ganin cewar ba zata canza -zani ba.

A halin yanzu dai Shugaba Biya bai kasafai yake bayyana a taron jama'a ba, baya yin tafiye-tafiye a cikin kasar ta Kamaru kuma ba zai halarci duk wani gangamin taron siyasa da za ayi don minshi ba.

A fagen harkokin kasa da kasa ma,Paul Biya ya barwa ministan harkoki wajen kasar damar wakiltarsa a taruka hadda na tarrayar Afrika.

Sai dai har yanzu shi ke da karfin fada a ji a siyasar kasar, kuma a yayinda wasu masu zaben suka gaji da mulkinsa kuma suke kokarin kauracewa zaben, wasu kuma goyon bayansa suke yi.

Da farko dai Paul Biya ya kasance wanda kowa ke alasan barka. A lokacin da Shugaba Ahmadou Ahidjo yayi murabus na bazata ya kuma mikawa Prime Minstansa mulki a wancan lokacin a shekarar 1982, yawancin 'yan Kamaru sun yi murna ganin cewar Shugaba Ahidjo ya shafe shekaru 22 yana mulkin kasar.

Sai dai tun kafin tafiya tayi nisa sai Paul Biya ya soma rayuwa irin ta kawa tare da kashe kudade abinda kuma ya jefa tattalin arzikin kasar cikin mawuywacin hali.

A shekarar 1990 bayan matsin lamba mai karfi, sai aka baiwa jamiyyun siyasa damar taka rawar a siyasar kasar.

Kuma jam'iyyar da aka soma kafawa ita ce Social Democratic Front ta Ni John Fru Ndi wacce ake ta babbar hammaya da ita, kamar yadda za a yi a mako mai zuwa. Sai dai kuma Paul Biya ya lashe duka zabukan da aka yi duk da cewar ana zarginsa da tafka magudi.

Kuma a wannan karon ma Paul Biya zai shiga zabe ne sakamakon garanbawul da aka yiwa kundin tsarin mulkin kasar mai cike da cece-kuce, inda aka soke batun wa'adin mulki sai biyu kacal.

Nfor Susungi wani dan Kamaru ne masannin tattalin arziki wanda kuma ya fasa takarar shugabancin kasar, saboda tunanin cewar babu wanda zai iya samun nasara akan Biya.

Yace "matsalar shugaba Paul Biya itace ya nemi hanyar da zai sauka daga kan mulki, idan ba haka ba wata guguwa na nan zuwa da zata kawar dashi".

Paul Biya zai fuskanci hammaya musamman daga babban dan adawa Fru Ndi da kuma sauran mutane 23 ciki harda manyan 'yan siyasa kamarsu Adamou Ndam Njoya, Garga Haman Hadji da kuma Bernard Muna. Amma dai yawancinsu basu da magoya baya sosai.

A ranar Lahadi tara ga watan Oktoba ne 'yan Kamaru zasu bayyana raayoyinsu a kwatunan zabe, amma da dama na ganin cewar ba za a samu wani sabon labari ba.