Matsalar tattalin arzikin Girka ta fi yadda aka yi hasashe

Hakkin mallakar hoto no

Kasar Girka ta ce ba za ta iya cimma wa'adin da aka diba mata ba, na zaftare gibin kasasin kudi a wannan shekarar da kuma a badi.

Duk da aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu masu tsauri da suka hada da rage kudaden da gwamnatin ke kashewa da kuma karin haraji.

Ma'aikatar kudin kasar ta ce, tattalin arzikin kasar na cikin matsanancin hali fiye da yadda aka yi hasashe.

wa'adin da ake son kasar ta cimma wani bangare ne na shirin ceton kasar, bisa yarjejeniyar da aka kulla da kungiyar tarayyar Turai da kuma hukumar lamuni ta duniya.