IOM ta fara kwashe 'Yan Afrika a Sabha

Kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya ta fara aikin kwashe wasu 'yan gudun hijira yan asalin Afrika daga garin Sabha na kudancin Libya.

'Yan gudun hijirar, su dubu daya da dari biyu, za a kai su kasar Chadi ne.

Malam Dauda Mamuda babban jami'in dake kula da ayyukan hukumar kula da kaurar jama'a ta IMO a Nijar, ya tabbatar da labarin.

Ya ce kimanin motoci sha biyar ne suka tashi a jiya, inda za su ratsa ta Nijar kafin isa Chadin.

'Yan Afrika da dama na korafin cewa, 'yan tawayen da yanzu ke mulkin galibin Libyar, suna kuntata masu bisa zargin cewa sojin haya ne na Kanar Gaddafi.