Steinman zai samu lambar yabo ta Nobel

Ralph Steinman Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ralph Steinman

Kwamitin da ke kula da kyautar Nobel ta duniya da ke kasar sweden, ya ce ba zai sauya matsayinsa na sanya dan kasar Kanadan nan, Ralph Steinman a jerin wadanda suka lashe kyautar Nobel ta bana ta kiwon lafiya ba, duk da cewa a yanzu sun gano cewa ya rasu tun kwanaki uku da suka gabata.

Sakataren kwamitin kyautar Nobel din Goran Hanson ya ce, sun san yana da cutar sankara, amma ba sa ware kowa saboda yana da wata cuta a lokacin da suke duba wadanda za su zaba domin basu kyautar.

Yace kuma sun yi fatan zai samu kyautar kafin ya rasu.

Mr Steiman ya lashe lambar yabon ne da binciken sa na kariyar lafiya da aka fi sani da immunology, tare da wasu mutanen biyu da suma suka yi wani binciken mai alaka da kariyar lafiya.