Za'a tashi marasa galihu daga bakin ruwa

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware game da kare muhalli a duniya.

Wannan ne kuma ya sa kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta shiyra taro na musamman, a kusa da unguwannin marasa galihu, da ke garin Fatakwal a Najeriya.

A cewar Kungiyar ta Amnetsy dai , an shirya taron ne , don sukar gwammnatin Jihar, game da tilasta wa wasu alummomi, dake zaune a Unguwannin da ke bakin ruwa, da aka fi kira da "Water Site", a cikin Garin Fatakwal.

Ko da yake, gwamnatin jihar na nuna cewa, ta yi niyyar yin hakan ne, don sake gyara Taswirar Garin, da kuma, kawar da bata-gari da ake zargin cewa sun yi kaka gida a unguwar.