Takaddama tsakanin China da Amurka

China da Amurka
Image caption An dade ana takun saka kan kasuwanci tsakanin Amurka da China

China ta mayar da martani a fusace ga shawarar da Amurka ta gabatar, ta neman a hukunta kasashen da ke karya darajar kudadensu da gangan.

A cewar ma'aikatar harkokin wajen Chinar, matakin zai keta ka'idojin cinikayya na kasashe.

Majalisar dattawan Amurkan dai ta amince a yi muhawara akan kudurin dokar, wanda ke neman kara kudaden haraji akan kayayyakin da ake sayowa daga kasashen da suka keta dokar.

Wasu kasashe na kukan cewa, kasar ta Sin na samun garabasa ta fuskar cinikayya da kawayenta, saboda ta karya darajar kudinta na Yuan.

Hakan ya sa irin kayayyakin da Chinar ke sayarwa kasashen waje sun kasance da arha.

Duk da yake kudurin da Amurka ta gabatar bai fito karara ya ambaci kasar China ba, sai dai babu tantama cewa Amurkan ta yi zagi a kasuwa ne.

Majalisar Dattawan kasar ta amince ta yi muhawara game da batun, kuma idan aka zartar da shi, to zai ladabtar da kasashen da suka rage darajar kudin su da gangan.

'Ita 'yar kasuwa ce kawai'

Sanata Chuck Schumer, na daga cikin 'yan majalisar Amurkan da ke son a gudanar da muhawara game da batun:

Kuma ya ce: "Akan batutuwa da dama, China na nuna ita 'yar kasuwa ce kawai. Tana amfani da dokokin kasuwanci ne idan za su amfane ta, idan ba haka ba kuwa ta yi watsi da su".

Kuma cikin shekaru da dama, Amurka na fushi da hakan, duk da yake bata dauki wani mataki game da batun ba.

Akwai gagarumin aiki nan gaba kafin kudirin ya zama doka, amma duk da haka, bai hana China mayar da martani mai zafi ba.

Ma'aikatun gwamnatin kasar guda biyu ne suka mayar da martani, abin da ke nuna irin harzukar da kasar ta yi dangane da gabatarda kudurin.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar, ta ce tana matukar adawa da kudurin.

Ita kuwa ma'aikatar Ciniki cewa ta yi babu adalci game da gabatar da shi, kuma ya sabawa duk wadansu dokoki na kasashen duniya.

'Yan kasuwar Amurka da ma 'yan siyasa da dama sun kwashe shekara-da-shekaru suna korafi game da yadda China ke rage darajar kudin ta.