Shugaban Iran ya soki Turkiya

Image caption Shugaban kasar Iran Ahmadinejad

Shugaba Ahmadinejad na Iran ya yi kakkausar suka a kan Turkiyya saboda amincewar da kasar ta yi da karbar bakuncin kafa wata na'urar gargadi a kan hari ta sama.

Kungiyar tsaro ta NATO dai ce za ta kafa na'urar gargadin.

A wata hira ta talabijin, Mista Ahmadinejad ya ce manufar girke na'urar a Turkiyya ita ce ba da kariya ga Isra'ila idan da yaki zai barke tsakaninta da Iran.

Mista Ahmadinejad ya ce babbar manufar girke na'urar da NATO ta yi a Turkiyya ita ce ba da kariya ga gwamnatin ta Yahudu;

"Suna so ne su hana makaman Iran masu linzami kaiwa yankunan da Isra'ila ta mamaye idan wata ran suka kai hari a kan Iran." In ji Ahmadinejad

Za dai a girke na'urar ne a garin Kurecik na lardin Malatya mai nisan kilomita dari bakwai daga kan iyakar Turkiyya da Iran.