Mummunan harin bam a Somalia

Somalia Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bam din ya ritsa da dalibai da ke shirin yin jarabawa

Mahukunta a kasar Somalia sun ce akalla mutane 70 ne suka mutu bayan da wani mummunan harin kunar-bakin-wake ya tarwatsa wani ginin gwamnati a Mogadishu, babban birnin kasar.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce wata babbar mota ce makare da nakiyoyi ta shiga ma'aikatar ilimi ta kasar, sannan aka tayar da bama-baman da ke ciki.

Kakakin kungiyar 'yan fafutuka ta al-Shabab, Sheikh Ali Mohamed Rage, ya shaida wa BBC cewa su suka kai harin.

Wakilin BBC a ma'aikatar ya ce ya ga gawarwakin jama'a a warwatse.

Ya ce wannan ne hari mafi muni da ya taba gani.

'Yawancinsu sun kone'

Wani jami'i a hukumar samar da agaji ta birnin Mogadishu, Ali Ruse, ya ce sun gano akalla gawarwakin mutane 65, yayin da wasu 50 suka jikkata.

"Har yanzu wasunsu na nan a kwance a kasa. Yawancinsu sun kone," kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Akwai jami'an gwamnatin rikon kasar da ke taro a wurin, sai dai babu tabbas ko suna cikin wadanda lamarin ya ritsa da su.

Rabon kasar ta Somalia da cikakkiyar gwamnati tun1991 - gwamnatin rikon wacce ke da raunin gaske na fafutukar neman iko da kungiyar 'yan fafutuka ta al-Shabab.

Al-Shabab, wacce aka ce ta na da alaka da kungiyar al-Qa'eda, ita ce ke rike da ikon kudanci da kuma tsakiyar kasar.

Ita kuwa gwamnatin rikon na da iko ne da birnin Mogadishu.

Karin bayani