Mummunan harin bam a Somalia

Somalia Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bam din ya ritsa da dalibai da ke shirin yin jarabawa

Kungiyar Islama mai fafitika a Somalia, Al Shabaab, ta ce ita ce ta kai harin kunar baki wake da bom ya kashe akalla mutane saba'in a Mogadishu, babban birnin Somalia, ya kuma raunata wasu mutanen fiye da tisi'in.

Harin shi ne mafi muni a tarihin kungyar na shekara biyar, kuma daya daga cikin wadanda suka fi muni a Somaliar a cikin shekaru ashirin.

Wata babbar mota ce shake da nakiyoyi ta aka tuka zuwa Ma'aikatar Ilmi Mai Zurfi ta kasar.

Wakilin BBC, Muhammad Dore, ya wannan shi ne hadari mafi muni da ya taba gani.

Ya ce, "Na ga gawawwakin da suka kone baje a kasa. Babban ginin ma'aikatar ya kone kurmus. Na ga kananan motoci suna cin wuta, manyan motoci suna cin wuta, da wasu sojoji a mace."

Wadanda suka shaida lamarin sun ce wata babbar mota ce makare da nakiyoyi ta shiga ma'aikatar ilimi ta kasar, sannan aka tayar da bama-baman da ke ciki.

Kakakin kungiyar 'yan fafutuka ta al-Shabab, Sheikh Ali Mohamed Rage, ya shaida wa BBC cewa su suka kai harin.

'Yawancinsu sun kone'

Wani jami'i a hukumar samar da agaji ta birnin Mogadishu, Ali Ruse, ya ce sun gano akalla gawarwakin mutane 65, yayin da wasu 50 suka jikkata.

"Har yanzu wasunsu na nan a kwance a kasa. Yawancinsu sun kone," kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Akwai jami'an gwamnatin rikon kasar da ke taro a wurin, sai dai babu tabbas ko suna cikin wadanda lamarin ya ritsa da su.

Rabon kasar ta Somalia da cikakkiyar gwamnati tun1991 - gwamnatin rikon wacce ke da raunin gaske na fafutukar neman iko da kungiyar 'yan fafutuka ta al-Shabab.

Al-Shabab, wacce aka ce ta na da alaka da kungiyar al-Qa'eda, ita ce ke rike da ikon kudanci da kuma tsakiyar kasar.

Ita kuwa gwamnatin rikon na da iko ne da birnin Mogadishu.

Karin bayani