Bikin ranar malamai ta Duniya

Image caption Hukumar bunkasa al'adu da kimiyya ta Majalisar Dinkin Duniya ce ta ware ranar malamai ta duniya

Yau Laraba, ranar malamai ta duniya, ranar da Hukumar bunkasa al'adu da kimiyya ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO ta ce an ware domin jawo hankalin al'umma ga irin rawar da malamai kan taka wajen bunkasa al'umma.

A fadin Najeriya kungiyoyin malaman za su yi taruka inda za'a yi jawabai akan halin da aikin malamanta yake ciki a Najeriya.

Sai dai kuma wannan buki na zuwa ne bana yayin da sha'anin ilimi ke fuskantar koma baya sosai.

A Najeriya wasu na danganta hakan ga irin halin da malamai da harkar ilimi ke ciki a kasar.

Ana dai dora alhakin lamarin akan hukumomi da kuma gwamnatoci.

Amma Jami'an gwamnati na cewa, idan bare na da sata daddawa ma nada wari.

kwashinan ilimi na jahar kaduna, Alh Mohammed Usman ya ce, Malaman makaranta da dama a jihar basu da kwarewar da ta kamata.

Ya ce dolene gwamnati ta sallami wadanda basu cancanta ba, kafin ta yi gyara a harkar illimi.