An gurfanar da wani jigon dan siyasa a Japan

Image caption Ichiro Ozama ne ya kafa jam'iyyar Democratic Party a Japan

An gurfanar da daya daga cikin 'yan siyasar Japan mai karfin fada a ji a gaban kotu, ana zarginsa da yin karan tsaye ga dokoki tara kudaden yakin neman zabe.

Dan siyasar, Ichiro Ozawa, na cikin wadanda suka kirkiri jam'iyyar Democratic Party mai mulki, kuma shi ne tsohon shugabanta.

An zarge shi ne da shugabantar rubuta bayanan samun kudi na karya da ma'aikatnsa suka yi.

An dai san Ichiro Ozawa da cuwa-cuwa a harkar siyasa abun da kuma yasa aka lakaba mai suna Shadow Shotgun.

Amma rawar da ya ke takawa a hakar siyasa ta fara fuskantar koma baya, ganin irin binciken da ake yi a kan sa game da yadda ya ke tara kudaden kamfe.

Tasirin Democratic Party

Wannan ne kuma ya sa aka tunbuke shi daga shugabancin jam'iyyar Demcratic Party, jim kadan kafin a gudanar da zaben da jam'iyyarsa ta lashe shekaru biyu da su ka wuce, abun da kuma ya katse mulkin kusan rabin karnin na mazan jiya a kasar.

A makon daya gabata ma, an samu na kusa da shi su uku da laifi.

Mista Ozawa, ya musanta aikata ba dai dai ba, inda ya ce 'yan siyasa ne kawai ke kokarin bata masa suna.

Ya ce mabanbanta ra'ayin jam'iyyarsa ne kawai ke kokarin bata masa suna, saboda irin alwashin da jam'iyyar ta sha na kawo gwamnatin kusa da jama'a.

Idan har ba'a same shi da laifi ba, Mista Ozama ne zai kalubalanci Pira Ministan Kasar, Yoshihiko Noda a zaben da za'a a yi a watan Satumbar badi.

A watan Afrailun badi ne dai kotu za ta yanke hakunci.