Tsohon shugaban Apple Steve Jobs ya mutu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mista Steve Jobs ya dade yana fama da cutar Cancer

Daya daga cikin mutanen da suka kirkiri kamfanin komfiyuta na Apple, Steve Jobs, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru hamsin da shida.

Mista Jobs na cikin manyan 'yan kasuwar da suka fi fice a duniya kuma shi ne ke da alhakin kawo sauyi a duniyar kimiyyar kere-kere ta hanyar na'urorin komfiyuta na Macintosh, da iPod, da iPad da kuma wayoyin salula na iPhone.

Steve Jobs Ya dai jima yana fama da cutar daji, wato cancer, kuma a watan Agusta ne ya sauka daga mukaminsa na shugaban kamfanin na Apple.

Da ya ke wani jawabi a watan Satumba na shekarar 2009, Mista Jobs ya tabo batun lafiyarsa, inda ya ce yi min dashen hanta.

Shugaba Barak Obama na Amurka ya bayyana shi da cewa mutum ne mai hangen nesa kuma daya daga cikin manyan Amurka.

Shugaba Obama ya ce duniya za ta yi koyi da irin fasahar da Mista Jobs ya kera,abun da kuma ya kawu sauyin ga hakar sardarwa a duniya.

Shugaban Microsoft Bill Gates ya bayanawa mutuwar babban abokin gasar sa a matsayin babban rashi a duniya, inda ya ce na baya za su amfana sosai daga abubuwan da ya kirkiro.

Mista Jobs ya mutu ne kwana daya da sabon shugaban Apple Tim Cook ya gabatar da wata sabuwar sumfurin wayar Iphone.

Karin bayani