An kama wasu dake shirin kashe Karzai

Gwamantin Afghanistan ta ce ta bankado wani shiri na kashe shugaban kasar Hamid Karzai.

Ta ce hukumar leken asiri ta kasar ta kama wasu mutane shida, cikinsu harda ma'aikata a fadar shugaban kasar.

Wasu daga cikin mutanen ana zargin suna da alaka da kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Haqqani wacce keda alaka da kungiyar A-Qaeda.

Lod`fullah Mashal, shi ne mai magana da yawun hukumar leken asiri ta kasar, ya kuma ce hukumarsu ta kama wata kungiya mai hadarin gaske wacce ta kunshi mutanen da ke da ilimi sosai.

Kungiyar na gudanar da ayyukanta ne a birnin Kabul, kuma ta kunshi malamai daga jami'ar birnin.

Babbar aniyarsu ita ce ta kashe shugaba Hamid Karzai.